Dujuman Bauchi Emirate

Dujuman Bauchi Emirate Fadar Dujuman Bauchi (Dr. Imam Abdurrahman Ibrahim Idris)

AN GABATAR DA NAƊIN SARAUTAR IMAM ABDULRAHMAN IBRAHIM IDRIS A MATSAYIN DUJUMAN BAUCHIA yau Juma'a, 3 ga watan Yuli, 2026...
03/07/2026

AN GABATAR DA NAƊIN SARAUTAR IMAM ABDULRAHMAN IBRAHIM IDRIS A MATSAYIN DUJUMAN BAUCHI

A yau Juma'a, 3 ga watan Yuli, 2026, an gudanar da bikin nadin sarautar Dujuman Bauchi Imam Abdurrahman Ibrahim Idris a Fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi, cikin gagarumin biki da ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na jihar.

Bikin ya gudana cikin tsari da natsuwa, inda aka shaida nadin sarautar tare da addu'o'i na musamman, inda mahalarta s**a taya sabon Dujuman Bauchi murna tare da yi masa fatan Allah Ya ba shi lafiya, hikima da ikon gudanar da wannan babban nauyi.

Bayan kammala bikin nadin sarautar, an gudanar da Hawan Doki, wanda ya ƙara wa bikin armashi da ɗaukaka. Dubban al'umma ne s**a fito domin kallon jerin gwanon da rakiyar sabon Dujuman Bauchi daga Fadar Sarki har zuwa gidansa da ke Jahun, cikin farin ciki da murna.

Masu ruwa da tsaki, malamai, hakimai, sarakunan gargajiya, jami'an gwamnati da sauran al'umma sun bayyana cewa wannan sarauta ta zo ne bisa irin gudummawar da Imam Abdulrahman Ibrahim Idris ya dade yana bayarwa wajen hidimtawa al'umma da kuma Jihar Bauchi.

An yi addu'ar Allah Madaukakin Sarki Ya sanya wannan sarauta ta zama alheri, Ya ba Dujuman Bauchi ikon yin adalci, hidima da kuma ci gaba da haɗa kan al'umma.

Allah Ya taya riƙo, Ya sanya albarka a sabon Dujuman Bauchi. Amin.

Dujuma Emirate
3rd July 2026
Dujuman Bauchi Emirate

Saƙon Godiya ga Mai Martaba Sarkin BauchiA Madadin Imam Abdurrahman Ibrahim Idris (Dujuman Bauchi), muna miƙa saƙon godi...
03/07/2026

Saƙon Godiya ga Mai Martaba Sarkin Bauchi

A Madadin Imam Abdurrahman Ibrahim Idris (Dujuman Bauchi), muna miƙa saƙon godiyarmu ta musamman ga Mai Martaba Sarkin Bauchi, Dr. Rilwanu Sulaiman Adamu (Sarkin Yakin Sarkin Musulmi), bisa irin karamci, alfarma da karramawar da ya yi masa ta hanyar naɗa shi sarautar Dujuman Bauchi.

Muna addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka masa da mafificin alheri, Ya ƙara masa lafiya, nisan kwana, hikima da ikon ci gaba da jagorantar Masarautar Bauchi cikin zaman lafiya, adalci da ci gaba.

Muna ƙara addu'ar Allah Ya ƙara ɗaukaka Masarautar Bauchi, Ya albarkaci jagorancin Mai Martaba Sarkin Bauchi, tare da sanya wannan sarauta ta zama alheri da ci gaba ga al'ummar Bauchi baki ɗaya.

A ƙarshe, inayi wa Dujuman Bauchi Abdurrahman Imam murna tare da fatan anyi taron naɗi lafiya. Allah ya kara taimakawa Ameen.

3rd July 2026
Dujuman Bauchi Emirate

SANARWA TA GAYYATAR RAKIYAR GODIYA TARE DA NAƊIN SARAUTAR MAI GIRMA DUJUMAN BAUCHI Assalamu alaikum warahmatullahi wabar...
01/07/2026

SANARWA TA GAYYATAR RAKIYAR GODIYA TARE DA NAƊIN SARAUTAR MAI GIRMA DUJUMAN BAUCHI

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh.

Mai girma Dujuman Bauchi Imam Abdurrahman Ibrahim Idris yana farin cikin gayyatar al’umma baki ɗaya, da masoya, abokai, da dukkan sauran al'umma, domin halartar rakiyarsa domin godiya da naɗin sarauta ta Dujuman Bauchi, zuwa fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi domin gabatar da godiya da nuna farin ciki bisa karamcin da Mai Martaba ya yi masa na ba shi sarautar Dujuman Bauchi.

Muna roƙon dukkan waɗanda za su samu damar halarta da su kasance tare da mu domin wannan muhimmin ziyara.

Za'a haɗu da ƙarfe 04:00pm na yammacin Juma'a 03th July 2026 a Kofar Gidan Marigayi Babban Limamin Masallacin Gwallaga dake Jahun

Allah Ya ƙara ɗaukaka masarautar Bauchi, Ya ƙara wa Mai Martaba Sarkin Bauchi lafiya da tsawon rai, Ya kuma albarkaci wannan sarauta ta Dujuman Bauchi.

Mun gode da halartar ku.

Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh.

IMAM ABDURRAHMAN IBRAHIM IDRIS (DUJUMAN BAUCHI) YA KARBI BAƘUNCIN AL’UMMA A FADARSA BAYAN DAWO DAGA AIKIN HAJJIA ranar J...
19/06/2026

IMAM ABDURRAHMAN IBRAHIM IDRIS (DUJUMAN BAUCHI) YA KARBI BAƘUNCIN AL’UMMA A FADARSA BAYAN DAWO DAGA AIKIN HAJJI

A ranar Juma’a 19 ga watan Yuni 2026, Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi, Imam Abdurrahman Ibrahim Idris (Dujuman Bauchi), ya zauna a fadarsa domin karɓar al’ummar Bauchi da s**a zo yi masa maraba bayan dawowarsa daga ƙasar Saudiyya tare da taya shi murnar kammala aikin Hajjin bana.

Mutane da ƙungiyoyi daban-daban sun samu damar ganawa da shi domin isar da saƙonninsu, taya shi murna da kuma nuna godiyarsu bisa irin ƙoƙarin da aka yi wajen gudanar da aikin Hajji cikin nasara. Daga cikin ƙungiyoyin da s**a kai ziyara akwai Takkan Nassarawa Community, JIBWIS Media Team, Hayatuddeen Organisation, Sha'irai Organisation, Ƙungiyar Masu Karatun Alƙur’ani, Jahun-Yanyamawa Organisation, IYACFOBA Organisation da kuma wasu daidaikun mutane.

A yayin ziyarar, wasu daga cikin ƙungiyoyin sun bayyana farin cikinsu da kuma addu’o’in fatan alheri ga Imam Abdurrahman Ibrahim Idris saboda jajircewarsa wajen hidimar alhazai da kuma jagorantar harkokin aikin Hajji na jihar Bauchi.

Haka kuma, wasu daga cikin masu ziyara sun gabatar da buƙatu da shawarwari daban-daban domin ci gaban al’umma. Imam Abdurrahman Ibrahim Idris ya saurari dukkan buƙatun da aka gabatar masa cikin natsuwa, inda ya tabbatar musu da cewa zai yi ƙoƙarin ganin an duba tare da aiwatar da abubuwan da suke da dama.

Ya kuma bayyana godiyarsa ga al’ummar Bauchi bisa wannan karamci da ƙaunar da s**a nuna masa, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kai da fahimtar juna wajen ci gaban al’umma.

Wannan ziyara ta kasance wata dama da ta ƙara ƙarfafa alaƙar dake tsakanin jagoranci da al’umma, tare da nuna yadda ake buƙatar sauraron muradin jama’a domin samar da kyakkyawan hidima.

Allah ya ƙara wa Imam Abdurrahman Ibrahim Idris lafiya da ikon ci gaba da hidimar al’umma.

Dujuman Bauchi Emirate
Friday 19 June 2026

AL'UMMA DAGA ƁANGARORI DA DAMA SUN KAWO ZIYARAR BANGAJIYA ZUWA FADAR MAI GIRMA DUJUMAN BAUCHI.A yammacin yau Alhamis 18 ...
18/06/2026

AL'UMMA DAGA ƁANGARORI DA DAMA SUN KAWO ZIYARAR BANGAJIYA ZUWA FADAR MAI GIRMA DUJUMAN BAUCHI.

A yammacin yau Alhamis 18 ga Junairu 2026 jama'a mabanbanta s**a kawo ziyarar bangajiya ga Babban Sakataren Hukumar Jindadin Alhazai ta Jihar Bauchi Imam Abdurrahman Ibrahim Idris (DUJUMAN BAUCHI) saboda dawowansa daga Aikin Hajji da ta gabata. Daga cikin waɗanda s**a samu damar kawo wannan ziyara akwai Masu Anguwanni wanda s**azo ƙarƙashin jagorancin Mai Anguwar Muazu, Malam Muhammad Tukur Sunusi inda ya fara da miƙa taaziyyar rasuwar marigayi Bunun Bauchi da kuma Mal. Shehu Jalam ga shi Dujuma. Sannan ya ƙara da godiya a madadin sauran masu Anguwanni na Albashi da shi Mai Girma Dujuma ya saka musu duk wata ba tare da sun roƙa bah. Daga ƙarshe sun nuna goyon bayansu ɗari bisa ɗari ga Mai Girma Dujuma a duk abunda yasa a gaba tare da masa fatan Allah ya tabbatar masa da muƙamin Shugaban Karamar Hukumar Bauchi.
Bayan masu Anguwanni akwai Kungiyar Media na gidan shi Mai Girma Dujuma wanda suma s**a gabatar da nasu gaisuwa tare da jinjina wa Dujuma na irin gudunmawar daya gabatar kafin Sallan lahiya na rabon tallafi ga iyaye Mata da masu Anguwanni, rabon Mashuna, dabbobin lahiya, da kuma goron Sallah daya basu duk da baya ƙasa amma haka ya aiwatar da irin waɗannan ayyuka. Sun nuna godiyar su matuƙa tare da alƙawarin cigaba da tafiyansa da kuma gudanar da ayyukan sa ba dare ba rana.
Matasa daga Anguwanni daban-daban suma sun samu zuwa don kawo koke-kokensu tare da gaisuwar bangajiya.
Daga karshe mai Girma Dujuma ya yaba wa masu Anguwanni tare da godiya kan ziyara da s**a kawo masa, ya ƙara da jinjina wa Ƴan Media na irin ƙoƙari dayaga sunayi tare da jan hankalinsu kan su ringa saka tsoron Allah a duk cikin lamarinsu.

DUJUMAN BAUCHI EMIRATE

ME YASA Dr. Abdurrahman Imam  IBRAHIM IDRIS YA DACE DA MAJALISAR TARAYYA?‘Yan uwa, mu yi tunani:1. YANA DA ILIMI –Dr. ne...
12/05/2026

ME YASA Dr. Abdurrahman Imam IBRAHIM IDRIS YA DACE DA MAJALISAR TARAYYA?

‘Yan uwa, mu yi tunani:

1. YANA DA ILIMI –
Dr. ne. Zai je Abuja ya yi muhawara da hikima, ba surutu ba. Zai kare Martabar Bauchi.

2. YANA DA TSORON ALLAH –
Sunansa Imam. Mutum ne mai Adalci. Ba zai ci Amanar ku ba.

3. YANA CIKINMU –
Ya san kowace Unguwa a Bauchi. Ya san Matsalolin mu . Shi ne zai kai Kukanmu Abuja.

Bauchi tana Bukatar mai Tarbiyyan Addini a zauren Majalisa. Dr. Imam shi ne zabi.

Mu tura shi Abuja ya yi mana Ihu Kada mu yi Shiru, da Kuma Wakilci Mai cike da Tsari .


.ImamAbdulrahmanMediaTeam

Address

Jahun Road Bauchi
Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dujuman Bauchi Emirate posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category