Giade Emirate

Giade Emirate Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Giade Emirate, Palace, Giade Local Government, Bauchi.

02/04/2026

Sarkin Yaran Giade

28/02/2026
GIADE EMIRATE COUNCIL PRESS26/02/2026SANARWAR HAWAN ƘARAMAR SALLAH (EID-AL-FITR) 1447AH/2026Majalisar Mai Martaba Sarkin...
27/02/2026

GIADE EMIRATE COUNCIL PRESS
26/02/2026

SANARWAR HAWAN ƘARAMAR SALLAH (EID-AL-FITR) 1447AH/2026

Majalisar Mai Martaba Sarkin Giade tana sanar da dukkan:
• Masu riƙe da sarauta
• Hakimai masu ƙasa
• Hakiman karaga

Cewa ana ci gaba da shirye-shiryen Hawan Ƙaramar Sallah na bana 1447AH/2026.

Hakimin karaga da zai yi hawa ya aiko da takarda a rubuce don tabbatarwa. Wanda ba zai yi ba, ba sai ya aiko ba.

Hakimai masu ƙasa kuwa, hawan Sallah wajibi ne a gare su, domin Mai Martaba bai ɗaukewa kowa ba.

A aiko da amsa daga yanzu zuwa 15/03/2026.

Allah Ya kai mu lokacin Sallah lafiya.

Secretary, Nura Wakili

Giade Emirate Council
Media & Publicity

26/02/2026
‎SAKON BARKA DA SHAN RUWA‎RANA TA (9)‎‎Sakon Barka Da Shan Ruwa Daga Uban Kasa Mai Martaba Sarkin Giade His Royal Highne...
26/02/2026

‎SAKON BARKA DA SHAN RUWA
‎RANA TA (9)

‎Sakon Barka Da Shan Ruwa Daga Uban Kasa Mai Martaba Sarkin Giade His Royal Highness Alh Mohammed Sabo Abdulkadir

‎Amadadin Mai Martaba Sarkin Giade HRH Alh Mohammed Sabo Abdulkadir Ya Mika Saƙon Barka Da Shan Ruwa Zuwa Ga Al’ummar Musulmi Na Duniya.

‎A Cikin Saƙon Na Barka Da Shan Ruwa Mai Martaba Sarkin Giade, Ya Yi Kira Ga Al'ummar Musulmi Cewa Da Su Ci gaba Da Ibada, Tare Da Yawaita Addu’a Da Ayyukan Akairi.

‎Mai Martaba Sarkin Giade HRH Alh Mohammed Sabo Abdulkadir Yayi Addu'a Tare Da Roƙon Allah Ubangiji Ya Sanya Albarka Cikin Rayuwarmu, Ya Karɓi ibadunmu, Ya yafe Mana Kura-Kuranmu, Kuma Ya Sa Mu Kammala Azumin Watan Ramadan Cikin Koshin Lafiya, Tare Da Farin Ciki Da Wadata Amin.

‎Giade Emirate Council
‎Media And Publicity

Aminan Juna Kenn 🤩✊🤩 Mai Girma Hakimin Cikin Garin Giade da Mai Girma Hakimin Warji  Allah ya Kara Lafiya da Nisan Kwana...
25/02/2026

Aminan Juna Kenn 🤩✊🤩
Mai Girma Hakimin Cikin Garin Giade da Mai Girma Hakimin Warji

Allah ya Kara Lafiya da Nisan Kwana ameen✊✊

Mai Martaba Sarkin Giade, Uban ƙasa, Mai adalci ga kishin al’umma, jagora na gari, ginshiƙin zaman lafiya da ci gaban ja...
30/01/2026

Mai Martaba Sarkin Giade, Uban ƙasa, Mai adalci ga kishin al’umma, jagora na gari, ginshiƙin zaman lafiya da ci gaban jama’a.

Allah ubangiji ya ƙara maka lafiya da nisan kwana albarkacin fiyayyen halitta annabi muhammad (saw) ameen.

Giade Emirate Council
Media And Publicity 30/01/2026.

Sabon Hakimin Cikin Garin Giade 👑 👑 👑 Allah ubangiji ya taya riko.
04/01/2026

Sabon Hakimin Cikin Garin Giade 👑 👑 👑

Allah ubangiji ya taya riko.

‎Mai Martaba Sarkin Giade, His Royal Highness Alh Mohammed Sabo Abdulkadir The First Emir Of Giade.‎‎Ya ziyarci Makarant...
02/01/2026

‎Mai Martaba Sarkin Giade, His Royal Highness Alh Mohammed Sabo Abdulkadir The First Emir Of Giade.

‎Ya ziyarci Makarantar Madarasatul Mu’azu Bin Jabal Littafizul Qur'an Makarantar (Malam Sarki Giade) Inda Makarantar Ta Gudanar Da Bikin Yaye Daliban Mutane Sittin Da Takwas (68) Wadanda S**ayi Saukar Alqur'ani Mai Girma.

‎Mai Martaba Sarkin Giade His Royal Highness Alh Mohammed Sabo Abdulkadir The First Emir Of Giade, Ya Nuna Farin Ciki Da Jindadi Ganin Yadda Yaran S**a Gudanar Da Karatun Alqur'ani Mai Girma Cikin Nutsuwa Da Girmamawa.

‎Mai Martaba Sarkin Giade HRH Alh Mohammed Sabo Abdulkadir Ya Kuma Jinjinawa Malaman Makarantar Ganin Yadda Suke Kokari Ba Dare Ba, Rana Ganin Sun Karantar Da Daliban.

‎Jindadin Wannan Abun Ne, Ma Yasa Mai Martaba Sarkin Giade Ya Bayar Da Gudunmowar ₦200,000, Tare Da Alkawarin Cewa Duk Lokacin Da Yake Gari Da Bazai Fasa Halattar Irin Waɗannan Tarukan Ba, Insha Allah.

‎Daga Karshe Malam Sarki Giade Yayiwa Mai Martaba Sarkin Giade Godiya Sosai Ganin Yadda Mai Martaba Ya Kawo Wannan Ziyarar Tare Da Bada Gudunmowa A Gidauniyar Makaranta Sannan Yayiwa Mai Martaba Addu'a Da Fatan Alkairi Tare Cewa Allah Ubangiji Ya Maida Mai Martaba Gida Lafiya Tare Da Daukaka Masauratar Giade Amin.

Habu Ibrahim Giade ✍️
‎Giade Emirate Council
‎Media Crew 01/01/2026.

Address

Giade Local Government
Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Giade Emirate posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category