28/09/2025
Malam Usman Suphi - Taƙaitacciyar Gabatarwa.
Malam Usman Adamu Ahmed (Suphi) ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Zaki ne a Jihar Bauchi, an haife shi a ranar 8 ga Satumba shekarar 1978. Suphi mutum ne mai hangen nesa, jajircewa, da kishin cigaban al’umma. Rayuwarsa cike take da nasarori, kuma abar koyi ce a fannoni daban-daban daga ilimi, aiki, gwagwarmaya, kasuwanci, siyasa, taimakon al'umma da dai sauran su.
Yayi karatu a FGC Azare, Abubakar Tatari Ali Polytechnic Bauchi, sannan ya wuce Bayero University Kano (BUK), inda ya samu nasarar zama Shugaban ƙungiyar Daliban Jihar Bauchi ta Ƙasa (President, NUBASS National Chapter) inda jagorancin sa ya samar da murya mai ƙarfi ga ɗaliban Bauchi a matakin ƙasa.
A fagen aiki, Malam Usman Suphi ya ƙware a fannin lissafi, haraji da binciken kuɗi. Ya fara aiki da kamfanin Deloitte & Touchè, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin binciken kuɗi na duniya inda yayi ƙaurin suna wajen aiki da ƙwarewa tare da riƙo da gaskiya da amana. A halin yanzu, shi ne Babban Jami’in Bincike (Chief Audit Executive) na babban kamfanin nan da ya shahara wajen gine-gine da sauran ayyuka a ciki da wajen Najeriya wato Julius Berger Nigeria Plc, haɗe da rassan sa da suke fadin ƙasa dama duniya baki ɗaya. Kafin nan ya riƙe muƙaman Chief Accountant da Head of Tax duk dai a kamfanin na Julius Berger Nigeria Plc.
Malam Usman Suphi ya shiga harƙoƙin siyasa da manufar kawo canji mai ma’ana da samarwa matasa ƴanci da murya a gwamnatance. Suphi ya bada gudumawa sosai a takarar tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi wato Alhaji Muhammad Nadada Umar (Zannan Misau) ta shekarar 2007. Suphi shine mutumin da ya ƙirƙiri Jam’iyyar NNPP kuma ya tallata ta har ta samu karɓuwa a faɗin ƙasa, inda ya riƙe mukaman Mataimakin Shugaban jam’iyyar na Ƙasa baki ɗaya. Ya tsaya takarar Gwamnan Jihar Bauchi a shekarar 2019, inda ya fito da tsari mai inganci kan ci gaban tattalin arziki, ilimi, da walwalar jama’a. A halin yanzu, yana daga cikin fitattun ƴan takarar Gwamnan Jihar Bauchi na kan gaba a zaɓe mai zuwa na 2027 ƙarƙashin tutar jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).
Malam Usman Suphi ya shahara wajen gabatarda ayyukan jinƙai da tallafa wa al’umma. Ya samar da guraben aiki na dindindin ga matasa ƴan Jihar Bauchi sama da mutum ɗari biyar (500+) a manyan hukumomin tarayya, hukumomin tsaro da kamfanoni a faɗin ƙasa. Ya ɗauki nauyin aurar da adadi mai yawa na mata marayu, inda yake biyan sadaki wa mazajen su, yayi musu kayan ɗaki, ya kuma basu kuɗi su ja jari. Kyautar motoci, babura, kujerun hajji da na umara da bada kyautar miliyoyin kuɗaɗe duk abubuwa ne da s**a riga s**a bi jinin Malam Usman Suphi. Baya ga haka, yana aiwatar da manyan ayyukan ci gaban al’umma, ciki har da ginin Cibiyar ICT/CBT mai ɗaukar dalibai 850 a Azare, domin buɗe ƙofofin fasaha da ilimi ga matasan Bauchi.
Malam Usman Suphi ya zama zakaran gwajin dafi a kowane bangare na rayuwar matashi, ya shigo siyasa da sabon salo na shugabanci mai haɗe da ƙwarewa, tausayi, hangen nesa da hidima wa al’umma.