02/10/2025
Happy Birthday Message Dedicated to My Mentor and Father, Dr. Bala Maijama’a Wunti
Alhamdulillah! Yau rana ce ta musamman a cikin rayuwata, ranar da nake tunawa da zagayowar haihuwata. Amma ban ɗauki wannan rana a matsayin ta kaina kawai ba, saboda na sadaukar da ita gaba ɗaya ga mutumin da ya zamo silar canji da nasara a cikin rayuwata — Ubangiji ya kaddara ya taimakeni da shi a lokacin da babu kowa a bangarena, lokacin da rayuwa ta yi min kunci, kuma nake bukatar agajin gaggawa. Allah ya azurta ni da wannan kyauta ta musamman, wato Dr. Bala Maijama’a Wunti.
Shi ne limamin canji da nasara a rayuwata, kuma a yau shi ne abin alfahari ga al’ummar Jihar Bauchi, wadanda suke yi masa addu’a da fatan ganin ya zamo Gwamnan Jihar Bauchi a shekarar 2027, in sha Allah.
Yau kuma shine karo na farko a rayuwata da na taɓa yiwa kaina fatan Happy Birthday, kuma ban yi hakan ba saboda kaina, sai don in nuna girmamawa da karramawa ta musamman ga Abbana, Jagora na, kuma kwarin gwiwa na, Dr. Bala Maijama’a Wunti.
Ya Allah, Ka tsawaita rayuwar Abbana Dr. Bala Wunti cikin lafiya da albarka, Ka ba shi ikon ci gaba da jagorantar al’umma zuwa ga cigaba, haɗin kai da nasara. Ka cika masa burinsa na alheri, Ka kare shi daga dukkan sharri, Ka ba shi ikon zama abin alfahari ga Bauchi da Najeriya baki ɗaya.
Allah Ka amsa addu’armu.
Happy Birthday to me – dedicated to my Father and Mentor, Dr. Bala Maijama’a Wunti.