Baycoz

Baycoz Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Baycoz, Political organisation, Bauchi.

02/08/2026

sanarwa

02/08/2026

Manoma suna godiya

munji kuma munbi kafar'ki kafan'mu MAMA Zainab Baban-Takko ko yau ko yanxu a shirye muke, nasarar" ki nasarar Al'umman b...
25/05/2026

munji kuma munbi

kafar'ki kafan'mu MAMA Zainab Baban-Takko

ko yau ko yanxu a shirye muke, nasarar" ki nasarar Al'umman bauchi cikin gari neh

kintaimaki Al'umma, kintaimaki Addini, kinyarda da Allah,

nasara yana tafe da ikon Allah.

pppp RRRR pppp

NASARA NASARA NASARA

23/05/2026

MATSAYAR HAJIYA Zainab Baban-Takko KAN MAGANAR CANJA JAM’IYYA

An bayyana cewa har zuwa wannan lokaci, Hajiya Zainab tana nan daram a cikin jam’iyyarta kuma babu wani mataki da ta dauka na sauya sheka zuwa wata jam’iyya daban.

Sai dai ta bayyana cewa tana ci gaba da kasancewa cikin addu’a da neman shawarwari daga masu ruwa da tsaki, magoya baya da kuma al’ummar da take wakilta domin tabbatar da duk wani mataki da za a dauka ya kasance mai amfani ga jama’a da ci gaban siyasa.

Hajiya Zainab ta jaddada cewa siyasa hidima ce ga al’umma, saboda haka tana mutunta ra’ayin jama’a tare da bude kofar karbar shawarwari daga mabiyanta da masu fatan alheri.

Ta kuma ce a halin yanzu babu wani tabbataccen matsayi na canza jam’iyya, amma duk wani abu da zai faru nan gaba zai kasance bisa shawarar Al'umma, fahimta da kuma abin da zai amfani al’umma baki daya.

Masu goyon bayanta sun bayyana cewa suna tare da ita tare da nuna kwarin gwiwa da amincewa da irin yadda take tafiyar da harkokinta cikin natsuwa, biyayya da kuma tuntubar jama’a.

20/05/2026

Khairan insha Allah

Road to federal insha Allah

MAMA Zainab Baban-Takko lafiya zaki gama da ikon Allah
20/05/2026

MAMA Zainab Baban-Takko lafiya zaki gama da ikon Allah



Assalaamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakaatuh.

Yau rana ce mai muhimmanci a wannan tafiya tamu, kuma ina kira ga dukkan ‘yan jam’iyya da masu kaɗa ƙuri’a da su fito cikin lumana, mutunci, da kishin jam’iyya domin gudanar da wannan zaɓe cikin gaskiya, haƙuri, da adalci.

Ina miƙa godiyata ta musamman ga duk waɗanda s**a tsaya tare da mu da addu’a, goyon baya, ƙarfafawa, da fatan alheri tun daga farko har zuwa wannan lokaci. Soyayya da karamcin da kuka nuna mana abu ne da ba za mu taɓa mantawa da shi ba.

A wannan rana, ina roƙon dukkan magoya bayanmu da masu fatan alheri da su kasance masu nutsuwa da girmama juna, ba tare da nuna fushi ko ɗaukar wani abu da zafi ba, komai sakamakon da Allah Ya ƙaddara. Siyasa ba ta fi zaman lafiya, mutunci, da haɗin kanmu muhimmanci ba.

Mun shiga wannan tafiya da niyyar hidima, gaskiya, da fatan kawo ci gaba mai amfani ga jama’a. Kuma muna da cikakken yaƙini cewa abin da Allah Ya rubuta shi ne mafi alheri. Idan nasara ta kasance tamu, Alhamdulillah. Idan kuma ba haka ba, har yanzu Alhamdulillah. Domin babu wani iko da ya fi na Allah, kuma babu abin da zai same mu face abin da Ya ƙaddara.

Ina addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanya alheri a cikin wannan rana, Ya ba mu zaman lafiya, haɗin kai, da abin da zai amfani al’umma da jiharmu baki ɗaya.

Nagode ƙwarai da gaske.
Allah Ya saka muku da alheri.

— Hajiya Zainab Baban-Takko
Aspirant,
Bauchi State House of Assembly
Bauchi Central Constituency
All Progressives Congress (APC)

12/05/2026

barayan mata Alkhairi neh

Damina uwar Alkhairi,

Al'ummar bauchi da kewaye, ga mai kishin'ku mai son cigaban'ku, mai burin kawo muku sauyi domin goben'ku

Allah ya idda nufin Alkhairi MAMA

Address

Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Baycoz posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share