02/09/2026
Yakubu Adamu Winning Team Ta Tallafa Wa Mata 50 Da Jari A Bauchi
Kungiyar Yakubu Adamu Winning Team, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Zainab Umar, ta tallafa wa mata 50 da jari da kuma kayan masarufi, a wani shiri na ƙarfafa mata da rage musu matsalolin rayuwa.
An gudanar da shirin ne a Unguwar Karofin Madaki, inda aka bai wa mata 50 tallafin da zai taimaka musu wajen farfaɗo da sana’o’insu da inganta rayuwarsu.
Da take jawabi yayin taron, Hajiya Zainab Umar ta bayyana cewa ta shirya wannan tallafi ne a madadin ƙawarta, Hajiya Aisha Yakubu Adamu Ph.D, matar ɗan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a ƙarƙashin jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), Dr. Yakubu Adamu Ph.D.
Tace zata cigaba da bayar da dukkan gudunmawarta wajen ganin Dr. Yakubu Adamu Ph.D ya samu nasarar zama Gwamnan Jihar Bauchi a zaɓen 2027, tare da burin ganin ƙawarta, Hajiya Aisha Yakubu Adamu, ta zama Uwargidan Gwamnan Jihar Bauchi (First Lady).
Taron ya samu halartar wasu daga cikin manyan jiga-jigan tafiyar Yakubu Adamu, da masu ruwa da tsaki, inda s**a yaba da ƙoƙarin Hajiya Zainab Umar wajen tallafa wa mata da kuma ƙarfafa musu gwiwar dogaro da kai.
Masu jawabi a wajen taron sun jaddada muhimmancin irin waɗannan shirye-shirye wajen ƙarfafa mata, bunƙasa ƙananan sana’o’i da inganta tattalin arzikin iyalai, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar ƙalubalen tsadar rayuwa.
Shirin ya kuma zama wata dama ta ƙara haɗa kan mata da masu goyon bayan tafiyar Yakubu Adamu, tare da ƙarfafa manufar tallafawa al’umma ta hanyar shirye-shiryen jin ƙai da ƙarfafa tattalin arziki.
Muryar Al'umma TV Daya Tamkar Dubu.
Sponsored Yakubu Adamu Shamsudeen Bala Mohammed Geo Barrister Mohammad Dan Sarki