27/05/2026
BARKA DA SALLAH DAGA HUKUMAR KWANA KWANA TA JIHAR BAUCHI.
A madadin dukkanin jami'an hukumar kwana-kwana ta jihar Bauchi, shugaban hukumar, Bldr Dauda B Pali MNIOB, Kachallan Pali, yana taya al'ummar musulmin jihar Bauchi murnar bikin sallar layyah wacce ake yi a yanzu haka.
Bldr Pali, yana kira ga al'ummar jiha akan kada su manta ta ɗaukar matakan kariya daga iftila'in gobara a lokacin da suke gudanar da hidimar bikin sallah, musamman kasancewar ita sallar layyah akan yi mu'amala da wuta wajen sarafa nama.
Iyaye mata su tabbatar da sun kashe wuta a duk lokacin da s**a gama amfani da ita, su kuma hana ƙananan yara mu'amala da wuta da sunan gasa nama ko kuma yin tsire.
Masu babbakan kai da ƙafa da kuma fata, su tabbatar da sun kashe wutar sosai a duk lokacin da s**a gama amfani da ita, kasancewar yanzu muna lokacin da ake yawan samun iska mai ƙarfi tana kaɗawa, sakamakon yanayin damuna da muke ciki.
A duk lokacin da ake buƙatar samun hukumar kwana kwana ta jiha, sai a kira ɗaya daga cikin wannan lambobin wayar, 07086463943 ko 09038352982.
Daga ƙarshe, shugaban hukumar yana roƙon Allah da Ya ci gaba da zaunar da jihar Bauchi lafiya da kuma kawo mata arziki mai albarka.
Allah Ya ja zamanin Mai Girma Gomnan Jihar Bauchi, Sen. Bala Abdkulƙadir Mohammed, Ƙauran Daular Uthmaniyya.
Allah Ya ja zamanin Mai Martaba Sarkin Bauchi, Dr Rilwanu Sulaiman Adamu .
Allah Ya ja zamanin Al'ummar Jihar Bauchi.