Assufiyyah MEDIA Concern AMCBP - 2027

Assufiyyah MEDIA Concern AMCBP - 2027 wannan kafa ce sadarwa na zamani domin kare muradu da yaɗa ayyukan Dan takarar Gwamnan jihar Bauchi a jam'iyar PDP Alhaji Usman Adamu Ahmed Suphi

17/07/2026

Labarin Da Dumi Dumi: kotu umarci hukumar INEC taci gaba da aiki da shugaban nin PDP ƙarƙashin jagorancin Abdurahman.

PDP ce jam'iya PDP Power 2027 PDP nasara in sha Allah
17/07/2026

PDP ce jam'iya
PDP Power 2027
PDP nasara in sha Allah

17/07/2026

Muna yi muku barka da juma'a

Idan har ya tabbata kotu ta hana mutanen PRP takara da ire iren su kuzo mu haɗa ƙarfi a jam'iyar PDP muyi malam Usman Ad...
16/07/2026

Idan har ya tabbata kotu ta hana mutanen PRP takara da ire iren su kuzo mu haɗa ƙarfi a jam'iyar PDP muyi malam Usman Adamu Suphi ba cuta ba cutar wa.

BAUCHI NA BUKATAR JAGORANCI MAI HANGEN NESAYayin da zaɓen Gwamnan Jihar Bauchi na shekarar 2027 ke ƙaratowa, lokaci ne d...
16/07/2026

BAUCHI NA BUKATAR JAGORANCI MAI HANGEN NESA

Yayin da zaɓen Gwamnan Jihar Bauchi na shekarar 2027 ke ƙaratowa, lokaci ne da ya dace al'umma su yi nazari kan irin jagorancin da suke fata domin ci gaban jiharmu.

Magoya bayan Malam Usman Adamu Ahmed Suphi, ɗan takarar Gwamna a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, suna bayyana cewa sun yarda da shi ne saboda irin halayensa na mutunci, ilimi, ƙwarewa da kuma kusancinsa da jama'a.

A cewarsu, Suphi mutum ne mai girmama kowa, mai sauraron jama'a, kuma mai hangen nesa kan yadda za a inganta ilimi, lafiya, noma, kasuwanci, samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa tattalin arzikin jihar Bauchi.

Sun yi imanin cewa, idan aka ba shi dama, zai yi aiki tare da kowane ɓangare na al'umma domin samar da shugabanci mai adalci, gaskiya da ci gaba.

Muna kira ga al'ummar Jihar Bauchi da su ci gaba da nazarin manufofi da halayen 'yan takara cikin natsuwa, tare da amfani da haƙƙinsu na zaɓe cikin lumana da bin doka.

Bauchi Sai Malam Usman Adamu Ahmed Suphi PDP (2027

Sarkin yaƙin neman zaɓen Dan takarar Gwamnan jahar Bauchi a jam'iyar PDP na shiyyar Bauchi ta arewa Alhaji Abdullahi Kud...
15/07/2026

Sarkin yaƙin neman zaɓen Dan takarar Gwamnan jahar Bauchi a jam'iyar PDP na shiyyar Bauchi ta arewa Alhaji Abdullahi Kuda yayi kira ga mambobin PDP da akayi watsi dasu a mai rogo da su zo su marawa Suphi domin nan ne PDP tagaskiya ba dodorido ba.

Zamu kawo muku cikakkiyar hirar....

Tafiyar Malam Usman Adamu Ahmed Suphi na Ci gaba da Samun Karɓuwa a Jihar Bauchi. Dubban mutane na shirin shiga tafiyar ...
15/07/2026

Tafiyar Malam Usman Adamu Ahmed Suphi na Ci gaba da Samun Karɓuwa a Jihar Bauchi. Dubban mutane na shirin shiga tafiyar Suphi

Tafiyar ɗan takarar Gwamnan Jihar Bauchi na jam'iyyar PDP, Malam Usman Adamu Ahmed Suphi, na ci gaba da samun karɓuwa daga al'ummar jihar, yayin da ake ci gaba da samun masu bayyana goyon bayansu ga tafiyarsa ta 2027.

Alhaji Audu Kuda, Sarkin Yaƙin Neman Zaɓen Malam Usman Adamu Ahmed Suphi, na ci gaba da gudanar da ganawa da masu ruwa da tsaki da kuma wayar da kan al'umma kan muhimmancin mara wa Malam Usman Adamu Ahmed Suphi baya domin ya zama Gwamnan Jihar Bauchi a zaɓen 2027.

A cewar masu shirya kamfen ɗin, jam'iyyar PDP na ci gaba da ƙarfafa tubalinta a faɗin jihar. Haka kuma, Alhaji Audu Kuda na shirin karɓar dubban sababbin mambobi daga jam'iyyun APC, ADC, APM da sauran jam'iyyu domin su shiga tafiyar Malam Usman Adamu Ahmed Suphi a ƙarƙashin tutar jam'iyyar PDP.

Sun bayyana cewa wannan ci gaba na nuna yadda tafiyar ke ƙara samun karɓuwa, tare da bayyana fatan cewa za a ci gaba da samun goyon bayan al'ummar Bauchi domin cimma manufofin da aka sa a gaba.

15/07/2026

PRESS RELEASE July 15, 2026RE: DAILY TRUST REPORT ALLEGING THAT PDP HAD NOT UPLOADED ITS PRESIDENTIAL AND VICE-PRESIDENT...
15/07/2026

PRESS RELEASE
July 15, 2026

RE: DAILY TRUST REPORT ALLEGING THAT PDP HAD NOT UPLOADED ITS PRESIDENTIAL AND VICE-PRESIDENTIAL CANDIDATES TO THE INEC PORTAL

The attention of the Peoples Democratic Party has been drawn to the report published by Daily Trust on Wednesday, 15 July 2026, titled “3 Parties Fail To Submit Presidential Candidates As INEC Shuts Portal,” in which it was alleged that the Peoples Democratic Party (PDP), under the leadership of His Excellency, Chief Nyesom Wike, was among the political parties that failed to upload the names of their presidential and vice-presidential candidates to the Independent National Electoral Commission (INEC) portal.

This claim is categorically FALSE, MISLEADING, and a GROSS MISLEADING OF FACTS.

For the record, the Peoples Democratic Party (PDP) successfully uploaded the names and particulars of its Presidential and Vice-Presidential candidates to the INEC nomination portal at exactly 11:50 a.m. on Thursday, 10 July 2026, in full compliance with the Commission’s requirements and within the stipulated timeline.

It is therefore surprising that a reputable newspaper such as Daily Trust chose to publish a report founded on unverified information attributed to an anonymous source without seeking confirmation from the party.

Journalism demands accuracy, fairness, and verification. Unfortunately, these basic principles were ignored in the publication, resulting in the dissemination of false information capable of misleading the public and creating an erroneous impression about the PDP’s compliance with the electoral process.

We therefore call on Daily Trust to immediately apologize and retract the inaccurate report, publish a correction, and accord this rebuttal the same prominence in the interest of fairness, professionalism, and responsible journalism.

Signed.

Hon. Jungudo Haruna Mohammed.
National Publicity Secretary

BAUCHI SABUWA 2027Jama'ar Jihar Bauchi masu kishin ci gaba, lokaci ya yi da za mu yi nazari kan irin shugabancin da muke...
14/07/2026

BAUCHI SABUWA 2027

Jama'ar Jihar Bauchi masu kishin ci gaba, lokaci ya yi da za mu yi nazari kan irin shugabancin da muke fata domin gina jihar da za ta samar da walwala, adalci da ci gaba ga kowa.

Malam Usman Adamu Ahmed Suphi ya shahara da ilmi, ladabi, biyayya ga al'umma da kuma kusanci da talakawa. Magoya bayansa suna bayyana cewa yana da hangen nesa na inganta ilimi, samar da ayyukan yi, bunƙasa tattalin arziki, ƙarfafa matasa da mata, da kuma inganta harkokin lafiya da ababen more rayuwa.

Mun yi imani cewa shugabanci na gari yana buƙatar gaskiya, riƙon amana, sauraron jama'a da aiki tare. Saboda haka, muna kira ga al'ummar Jihar Bauchi su yi nazari a kan manufofi da cancantar 'yan takara tare da ba da goyon bayan wanda s**a ga ya fi dacewa da burinsu.

Mu haɗa kai domin gina Bauchi da ci gaba, zaman lafiya da walwala ga kowa.
Bauchi Sabuwa 2027!

Address

Assufiyya ICT And Humanitarian Centre, New Maiduguri Bypass Azare
Azare

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Assufiyyah MEDIA Concern AMCBP - 2027 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share