Hon. Alhaji Yahaya S/Fagon for Anka constituency 2027 NDC

  • Home
  • Nigeria
  • Anka
  • Hon. Alhaji Yahaya S/Fagon for Anka constituency 2027 NDC

Hon. Alhaji Yahaya S/Fagon for Anka constituency 2027 NDC Hon.Alhaji Yahaya S/Fagon is a visionary leader and grassroots mobilizer, and passionate advocate

Allah kabamu nasara daga sama har kasa🙏
14/07/2026

Allah kabamu nasara daga sama har kasa🙏

‎Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.‎Ya ku al’ummar Anka da kewaye, da girmamawa da cikakkiyar tawali’u nake...
24/06/2026

‎Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.
‎Ya ku al’ummar Anka da kewaye, da girmamawa da cikakkiyar tawali’u nake sake tabbatar muku da cewa wannan tafiya tamu tafiya ce ta gaskiya, hidima, da ceto muradun jama’a.
‎Na san irin wahalhalun da al’ummar mu ke ciki na tsaro, talauci, rashin aikin yi, matsalolin ilimi, da ƙalubalen rayuwa da s**a dabai baye gidajen mu da ƙauyukan mu. Wannan ne ya sa na yanke shawarar tsayawa domin in zama murya ta talaka, kariya ga marasa ƙarfi, da wakilin da zai tsaya tsayin daka wajen kare martabar Anka.
‎
‎Ina miƙa hannu gare ku matasa, mata, dattawa, manoma, 'yan kasuwa da ɗaukacin al’umma mu haɗa kai domin canjin da zai amfani kowa.
‎Lokacin aiki ya yi. Lokacin wakilci na gaskiya ya yi.
‎Da yardar Allah, tare da goyon bayanku, Anka za ta yi alfahari da zabinta.
‎Hon. Alhaji Yahaya S/fagon Barayar Zaki
‎Dan Takarar Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Anka Constituency
‎Murya ta Talaka, Gatan Al’umma
‎
‎
‎
‎
‎
‎

Cikin alhini da damuwa nake jajantawa al'ummar Tungar Godai bisa mummunar harin da ya jawo garkuwa da wasu daga cikin al...
23/06/2026

Cikin alhini da damuwa nake jajantawa al'ummar Tungar Godai bisa mummunar harin da ya jawo garkuwa da wasu daga cikin al'umma. Muna addu'ar Allah Ya kiyaye rayukansu, Ya kubutar da su cikin koshin lafiya.
Abin takaici ne yadda al'ummar Bagega Ward s**a shafe kwanaki 53 babu shiga babu fita, yayin da kasuwar Rafin Gero ta kusan watanni 4 ba ta aiki saboda matsalar tsaro. Haka ma akwai sauran kauyukan Anka da ke ci gaba da rayuwa cikin tsoro da kunci.
Muna kira da babbar murya ga Gwamnati da hukumomin tsaro da su tashi tsaye su kawo karshen wannan bala'i. Al'ummar Anka ba sa bukatar alkawura kawai, suna bukatar ingantaccen tsaro, kariyar rayuka da dukiyoyi, da matakan gaggawa da za su dawo da zaman lafiya.
Lokaci yana tafiya. Kafin lokaci ya kure, a ceci al'umma.
Allah Ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa, Ya kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su, Ya kare daukacin karamar hukumar Anka da Zamfara baki daya.
Hon. Alhaji Yahaya S/Fagon Barayar Zaki
Dan Takarar Kujerar Majalisar Dokokin Jihar Zamfara (Anka Constituency), NDC

18/06/2026

Allah Bamu zaman lafiya a ƙauyukan mu na Anka da jaha, kasa baki daya🙏

Address

Barayar Zaki Area Of Anka
Anka
890001

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hon. Alhaji Yahaya S/Fagon for Anka constituency 2027 NDC posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share