24/12/2025
Farfesa Muhammad Ali Pate mutum ne da muke masa kyakkyawan zaton Samar da Mafita ga al’umman da s**a Gaza samun romon dimokuraɗiyya.
Nazari kan ayyukansa na nuna cewa yana tafiya da salo na daban da yawancin ’yan siyasar da muka sani. Bayayin siyasa ta rabon kuɗi kawai ga wasu ’yan kaɗan, yanayin abun da jama'a da dama zasu amfana ne gaba Daya, yayin da al’umma gaba ɗaya ke ci gaba da fama da talauci da neman Mafita cikin sha'anin rayiwa, yanada kyau mu mayar da hankali mu gurin wannan bawan Allah, Saboda shi Abin da ya fi bai wa muhimmanci shi ne samar da ayyukan yi ga matasa, da samo hanyoyin da zai bunƙasa tattalin arziki, ƙarfafa dogaro da kai da kuma gina al’umma mai tunani Mai kyau, Kuma yin Hakan Tabbas ya kan kau da fatara, ya wanzar da zaman lafiya.
A duk ayyukansa ana ganin tsari, tausayi da kuma ƙudurin rage wa jama’a wahala da ƙunci.
In Ka dubi bangaren kiwon lafiya, manufofinsa sun ta’allaka ne wajen sauƙaƙa rayuwar jama’a. Tun bayan shigan sa ofis, ya bullo da sabbin tsare-tsare da za su inganta harkar lafiya, su samar da ayyukan yi, tare da ƙara wa gwamnati kuɗaɗen shiga.
Duk inda Farfesa Pate ya jagoranta, sai anga sauyi mai amfani ga jama’a. Saboda haka, Matukar munason Ganin sauyi Mai amfanar wa wajibi ne al’umma su gane kimarsa da cancantarsa ta shugabanci, mu mara masa baya, mu ba shi dama tare da yi masa addu’a. In sha Allah, Jihar Bauchi za ta shaida sauyi na ban mamaki.
Abdul'aziz Musa Sa'id
Pate Media Center
December 24-2025