31/10/2023
SHUGABANCI DA AMANA.
A ƙarshen kowanne irin al'amari gaskiya ita ce ke tabbatuwa. Ya kamata a ba ku shawara kuma a gaya muku gaskiya a matakin ƙarshe, ko hakan yasa ku ƙarasa cikawa da imani, amma ba a dinga ƙoƙarin kare ɓarnar da kuka yi ba. Yin shiru akan ɓarna ko kuskuren shugabanni hakan yana nuna tsoro da kwaɗayin abin duniyar da wasu suke samu kada ya ƙare. Sun manta cewa rayuwar kowa tana ga Allah maɗaukakin sarki.
Manzan Allah (saw) ya faɗi wasu halaye guda uku 3 ya ce "duk wanda yake da su a cikin halayensa to haƙiƙa shi munafiki ne. Ko da yayi sallah, yayi azumi, ko da yayi hajji yayi ummara, ko da ya ce shi musulmi ne.
Mu riƙe mana,
Mu yi gaskiya,
Mu cika alƙawari.
Babu hujjar da zata sa wani ya kwashe dukiyar ku domin biyan buƙatar kansa, ku kuma ku zo kuyi ta girmama shi dan rashin sanin ciwon kai da rashin zuciya. Ko da yake su shugabanni addu'a suke buƙata, sannan a gaya musu kuskurensu a nasihance, amma hakan ba zai hana ku yin Allah wadai da abin da s**a aikata na rashin daidai ba.
Allah ka shiryemu, ka bamu shugabanni nagari.